Thursday, 4 April 2013




An shiga rana ta uku ta gasar karatun Al-kur'ani mai girma karo na 29 a Iran


A yau talata ne aka shiga rana ta uku ta gasar karatun Al-kur'ani mai girma karo na ashirin da tara da aka saba gabatarwa shekara-shekara a Jamhuriyar Musulunci Ta Iran, tare da halartan mahaddata, makaranta, da masu tafsirin Al-kur'ani daga kasashen musulmi daban daban......

code:102569
2012/6/19  21:49
Na duniya.
A bana ana gabatar da wannan gasar ne a babban dakin taro na Milad Tower wani babban gini dake tsakiyar birnin Tehran.
Bayan kammala gasar mahalarta suna kai ziyara ta musamman ga jagoran juyin juya hali na Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei inda yake gabatar da jawabi gare su.
Ga wata tsaraba da muka kalato na wasu hotunan yadda wannan gasar take gudana a halin da ake ciki a Tehran babban birnin kasar ta Iran.

No comments:

Post a Comment