Tuesday, 29 July 2014

onathan ya yi tir da hare-haren kano

An sabunta: 28 ga Yuli, 2014 - An wallafa a 23:53 GMT
A can jihar Adamawa kuwa sama da mutane 50 ne rahotanni suka ce an kashe ciki har sojoji hudu.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi tir da jerin hare-haren ta'addanci da aka kai kwannannan a jihohin kano da Adamawa kazalika da sace Sarkin Kolofata da matar mataimakin firayin ministan Kamaru da aka yi.
Shugaban ya bayyana haren-haren bom da aka kai a birnin Kano cikin sa'o'i 24 a dai dai lokacin da musulmi ke bukukuwan sallah karama, a zaman masu ta da hankali, na rashin imani kuma abin kyama.
A cikin wata sanarwa wadda kakakinsa Dr. Rueben Abati ya sa wa hannu, Shugaba Jonathan ya ce amfani da 'yan mata wajen kai harin kunar bakin wake, wata sabuwar sabga ce ta aikin rashin imani da wadanda ya kira 'yan ta'adda suka fito da ita, kuma manuniya ce karara ta rashin sanin darajar jinsin mace.
Da misalin karfe goma na safiyar Litinin ne wata mata 'yan kunar bakin wake ta kutsa a cikin wani taron masu sayen kalanzir a wani gidan mai da ke kanon inda ta tayar da bam din da ke jikinta, abin da yayi sanadin mutuwarta da kuma wasu mutane hudu.
Kimanin sa'oi uku bayan haka kuma wata 'yan kunar bakin waken da 'yan sandan suka ce kimanin shekarunta 18 ta tayar da nata bam din a harabar kasuwar baje-koli duk dai a Kano inda ta halaka kanta tare da raunata wasu mutane shida.

No comments:

Post a Comment