Rariyar likau mai saukaka amfani da shafi
Ana tsangwamar masu hijabi a Kano
An sabunta: 12 ga Agusta, 2014 - An wallafa a 00:53 GMT

Yankin da aka kai hari a Kano
Tun bayan da wasu 'yan mata suka
kai wasu hare-haren kunar bakin-wake a jihar Kano dake arewacin
Nijeriya, jama'a suka fara dari-dari da duk wasu 'yan matan dake sanye
da hijabi.
Hakan dai ta sa wasu 'yan matan da suke sanya
Hijabi suke fuskantar tsangwama da kyama, yayinda wasu kuma suka ce sun
dakatar da sanya hijabi a yanzu.Mutane dai na cewa suna nuna rashin amincewar ne kasancewar duka 'yan matan da suka kai hare-haren kunar bakin-wake a watan jiya suna sanye da hijabai ne.
Yanzu haka dai ana sa ido da binciken kwakwaf ga duk wata mace musamman matashiya dake sanye da hijibi a kasunni da ofisoshi a Kano.
Kari a kan wannan labari

No comments:
Post a Comment